Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, gwagwarmayar da al'ummomin larabawa suke yi a cikin wadannan lokuta domin nuna rashin amincewa da salon mulkin zalunci da ke tafiyar da kasashensu yana da dangantaka da addinin muslunci bisa la'akari da taken da ake rerwa a lokutan zanga-zanga.
Kare kai daga harin makiya daya ne daga cikin hakkokin mutum, amma kur’ani mai tsarki duk da karfafawar da ya yi wajen kare kai, ya jaddada wajabci kan kada a wuce iyaka wajen kare kai. Haka nan kuma kur’ani ya nusar da mu cewa, kafin yin kira ga makiya addinin musulunci zuwa ga addinin Allah, kada a dauki takobi a kansu, kada a fara yaki da su, a lokacin yaki kuma kada a taba kanan yara da mata da tsoffi,kare hakkokin dan adam a lokacin yaki, sai dai wanda ya yi shishigi a kan musulmi ne kawai za a yaka.
Wadannan ayoyi suna umurtar musulmi da su mayar kwatankwacin abin da mushrikan makka suka yi a kansu, domin kuwa sun fitar da musulmi daga gidajensu da kuma birnin, sun mayar da su ‘yan gudun hijira, sun saka musulmi cikin azaba ta fitina, inda Allah ya bayyana wannan fitar da aka jefa musulmi a cikinta da cewa tafi yaki tsanani.
Ko da yake Allah madaukakin sarki ya ce da musulmi kada su yaki mushrikai a dakin ka’aba saboda alfarmar wannan wuri mai tsarki, sai dai idan mushrikan ne suka fara yakar musulmi a cikinsa, idan kuwa har suka kai hari kan musulmi a masallaci mai alfarma, Allah madaukakin sarki ya ba musulmi damar su kare kansu ta hanyar yakar kafirai mushrikai, domin kuwa a wannan lokacin musulmi suna matsayin masu kariyar kai ne, ba masu kai harin yaki ba.
840656