IQNA

Faderation Din Australia Shi Ne Babbar Madogara Ga Musulmin Kasar

17:14 - August 11, 2011
Lambar Labari: 2168997
Bangaren siyasa da zamantakewa, Domin tattabar da adalci da kawar da zalunci da daukaka kalmar da kawar da azzaluman jagorori a cikin al’umma ne ake yin jihadi daidai da sharudda da aka shimfida kan haka a musulunci.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin malaman addini na kasar ya bayyana cewa, Manufar jihadi a musulunci ba ‘yan kasanci ko kabilanci ko wariya neman ganima ba ce, babbar manufar jihadi a musulunci ita ce tabbatar da kalmar Allah da fadarsa a bayan kasa, kawo karshen fitina da zalunci da shirka da kafirci da surkulle, du kuwa da cewa dukkanin yakokin da musulmi suka yi a lokacin ma’aiki, sun yi su ne domin kare kai daga masu cutar da muslunci da musulmi, an fara yakin ne a kan ma’aaki da mabiyansa, ba su ne suka fara yaki ba.

Domin kuwa sun dauki tsawon shekaru ana cutar da su ana yakar ba su ce komai illa isar da sakon Allah madaukakin sarki, tare da jurewa wahalwahu da azabtarwa saboda Allah, amma bayan hijirar manzo an yi wa wadanda suka yi imani izini da su yi yaki domin su kare kansu saboda zaluncin da ake yi musu ya kai matukarsa, to wannan shi ne jihadi a musulunci kamar yadda manzo ya koyar da musulmi.

musulmi ba su da izinin yin yaki a cikin wadannan watanni, an kuma kulla yarjejeniya da su a cikin wadannan watanni babu yaki, saboda haka sai suka yi amfani da wannan damar domin shishigi kan musulmi, saboda sun san cewa dai ba za a rama ba, to amma Allah madaukakin sarki ya umurci musulmi da su mayar da kwatankwaci akan mushrikai, domin su kare kansu daga shishiginsu.

837620

captcha