Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wakilin kungiyar jihadul islami abirnin Tehran Abu Sharif ya bayyana cewa, fadakar al'ummar musulmi da kuma mikewarsu gami da kama hanyar faduwar yahudawan sahyuniya shi ne abu mafi muhimmanci ga al'umma a wannan lokaci, domin kuwa ta haka ne sauran al'ummomin duniya za su samun zaman lafiya da kuma kwanciyar hanakali, bisa la'akar da cewa yahudawan sahyuniya su ne ummul haba'aisin duk wani tashin hankali a duniya, da kuma yankin baki daya.
A bangare guda guda kuma wani rahoton ya ce, Babban baitul-malin kasar Amurka ya ce za'a dauki akalla shekaru biyu a nan gaba kafin tattalin arkin kasar ya iya mirmijewa daga halin tangal-tangal da ya fada a sakamakon mummunan salo na jari hujja da kasar ta dogara da shi.
Jacob Humberger wani dan siyasa kuma masani tsari tattalin arziki a kasar ta Amurka, ya ce gwamnatin kasar ce ke da alhaki dangane da yadda lamurra ke ci gaba lalacewa a kasar, wannan kuwa a sakamakon kasawarta na daukar matakan da suka dace domin tunkarar wannan matsala, duk da cewa tuni aka yi hasashen cewa haka za ta iya faruwa a kasar.
Kamar dai yadda wasu alkaluma da ma'aikatar kwadago ta kasar ta fitar a karshen watan yunin da ya gabata ke nunawa, akalla mutane milyan 14 da dubu dari daya ne ke zaman kashe wanda a kasar ta Amurka, kuma babu alamun yiyuwar shawo kan wannan matsala ta rashin aikin yi a cikin gajeran lokaci.
841829