Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki a taron baje koli da ke gudana a birnin Tehran wanada aka tarjama a cikin harshen Pashtu da kua wasu litatafa da aka tarjama ko rubuta su a cikin wannan harshen.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, a babban masallacin Imam Khomeini (RA) an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki a taron baje koli da ke gudana a birnin Tehran wanada aka tarjama a cikin harshen Pashtu da kua wasu litatafa da aka tarjama ko rubuta su a cikin wannan harshen wanda akasarin masu Magana da shi mabiya addinin muslunci ne.
An saba gudanar da wannan abje koli ne a cikin wannan wata, hakika yanayin watan Ramadan mai alfarma ya banbanta da dukkanin sauran lokuta da musulmi suke gudanar da ayyukan ibada a cikinsa, domin kuwa lokaci da Allah madaukakin sarki yake kwararo rahamarsa da albarka a kan bayinsa, lokaci ne da Allah yake yin gafara ga bayinsa, a cikinsa ne ke da dare guda daya wanda yafi watanni dubu daya daraja da albarka, wanda aikin ibada a cikinsa yafi aikin ibada a cikin watanni dubu daya.
A cikin wadannan kwanaki 30 na wannan wata mai albarka ne mutum ke samun tarbiyar da za ta rike tarbiyar da ruhinsa ya samu a cikin sauran watanni 11 na shekara. Manzon Allah (SAW) ya umurce mud a kada mu yi sakaci da wannan babbar da ma da Allah (SWT) ya ba mu. Allah yasa mu dace da dukkanin alkhairan da Allah ya saya a cikin wannan wata.
841746