Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da ke cewa, daruruwan musulmi ne mabiya tafarkin sunna da shi'a suka gudanar da sallar jama'a domin samun hadin kai mai dorewa tsakanin al'ummar musulmi wadda aka udanar a kasar Syria a karkashin jagorancin malamin addini kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar.
A wani labarin kuma na daban wakilin kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan matsayin gwamnatocin kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa da Jamus dangane da rikicin da ke faruwa a Siriya.
A taron manema labarai da ya gudanar bayan zaman tattaunawa da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan rikicin kasar Siriya a jiya alhamis; wakilin kasar ta Siriya Basshar Ja'afari ya furta cewa: babban abin bakin ciki ne yadda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya zame yana nuna wariya tare da rashin adalci kan al'amuran da suke gudana a duniya saboda matsin lamban wasu manyan kasashen yammacin Turai.
Ajja'afari ya fayyace cewar babu wani lokaci da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwarsa kan zaluncin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ke gudanarwa kan al'ummar Palasdinu amma kan rikicin kasar Siriya yana watsa rahotonnin karya marassa tushe.
Ajja'afari ya kara da cewa; wasu mambobin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin ganin kasar Siriya ta kama hanyar zama irin kasar Libiya, to amma bakar aniyarsu ba zata taba cimma nasara ba.
841652