IQNA

Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki A Birnin Sandiago Na Kasar Amurka

17:03 - August 13, 2011
Lambar Labari: 2169911
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki a birnin Sandiago na kasar Amurka tare da halartar wakilan cibiyoyin addinin muslunci na kasar daga sassa daban-daban.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo na icsd.org cewa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki a birnin Sandiago na kasar Amurka tare da halartar wakilan cibiyoyin addinin muslunci na kasar daga sassa, kuma ga dukkanin alamu a wanna karo gasar za ta samu ci gaba fiye da sauran lokuta.
Duniyar da muke rayuwa a cikinta, tamkar wata kasuwa ce, mu kuma tamkar wasu 'yan kasuwa ne dole ne mu saka dukiyoyinmu a matsayin jarukanmu na kasuwanci, mu saye da sayarwa, jarin namu kuwa shi ne rayuwa da samartaka, hankali da tunani, ilimi da iko da dukkanin daar da muke da ita wadda Allah ya ba mu a cikin rayuwa.
A cikin wannan kasuwa wasu suna cin riba, kuma suna kaiwa ga sa'ada ta duniya da lahira, yayin da kuma wasu suke samun karaya acikin harkarsu ta kasuwanci, kamar mai sayar da kankara ne, idan bai sayar da ita ba to za ta zama ruwa, kuma zai rasa jarinsa.
A cikin wurare da dama a cikin kur'ani mai tsarki, an yi nuni da hakan, inda a cikin surat Saf aya ta 9 aka siffanta imani da jihadi a matsayin tijara.
841605
captcha