IQNA

An Fara Gudanar Da Baje Kolin Littafai Na Watan Ramadan A Kasar Begium

14:23 - August 14, 2011
Lambar Labari: 2170512
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje koli na littafan muslunci a birnin Liege na kasar Belgium tare da halartar cibiyoyin buga littafai na kasar da ma wasu daga cikin mabiya addinai da suke bukatar sanin wani abu kan muslunci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da wani baje koli na littafan muslunci a birnin Liege na kasar Belgium tare da halartar cibiyoyin buga littafai na kasar da ma wasu daga cikin mabiya addinai da suke bukatar sanin wani abu kan muslunci domin kaucewa fadawa cikin abin da ake son nuna musu na bata duk wata sura ta musulunci a kasar.

Allah ne kawai ake rusanawa a matsayin ubangiji, babu wani mahaluki da zaim iya maye gurbin Allah madaukakin sarki, komai ikonsa da dukiyarsa da karfin jikinsa Wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe,kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.

Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yana aiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana ba su sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam.

A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi Musa ya safkar da Injila ga annabi Isa, shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad, idan da gaske suna neman gaskiya ne, to wajibi ne su yi iani da annabi Muhammad da sakon da ya zo da shi daga Allah.

842233
captcha