Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, dubban mutane musulmi suna gudanar da sallar Juma'a amasallacin Qods mai alfarma a cikin watan Ramadan duk kuwa da matakan takurawa da yahudawan sahyuniya suke dauka na hana musulmi gudanar da ayyukansu an ibada a wannan wuri mai albarka.
Daya daga manyan ayyukan zalunci shi ne rafkana daga ubangiji, alhali babu wani lokaci da mutum ba ya karkashin ikon ubangiji, kuma yana gani da sauraren dukkanin ayyukan mutum, ba ma mutum ba wanda adadinsa ko alama bai kai halittun Allah da ke cikin sammai da kassai ba, wadanda su ma Allah yana tare da su, yana da masaniya kan dukkanin abin da suke yi, bil hasali ma shi ne ke ikon tafiyar da su baki daya.
Babu abin da ke buya ga Allah, a cikin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, hatta ma jariri da ke cikin mahaifa samuwarsa tana hannun Allah, shi ne yake tsara halittar jinjiri a cikin mahaifa har ya kai lokacin da zai gama girma a haife shi, ya raya shi ya kare shi, lallai Allah shi ne mai hikima.
842248