Bangaren kasa da kasa, wani malamin jami'a a bangaren nazari kan harkokin muslunci a jami'ar Hamburg da ke kasar Jamus ya bayyana cewa ya zama wajibi a samara da wata majalisa, wadda za ta hada dukaknin addinai na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto an bayyana cewa, wani malamin jami'a a bangaren nazari kan harkokin muslunci a jami'ar Hamburg da ke kasar Jamus ya bayyana cewa ya zama wajibi a samara da wata majalisa, wadda za ta hada dukaknin addinai na duniya da nufin samun karfafa juna da kuma fahimta a tsakanin dukkanin bangarorin addinai.
Sau da yawa wasu kan gina akidunsu bisa dogaro da zahirin ayoyi masu kama da juna sai hakan ya kai su ga suranta Allah madaukakin sarki tamkar wani mutum ko wani abun halitta, alhali kuwa irin wadannan ayoyi na kur'ani suna bukatar tawili, kamar yadda wannan ayar ta ce babu wanda ya san tawilinsu sai Allah da kuma wadanda suka tsaga ilimi, wato annabawa da kuma wasiyyansu.
Da kuma wasu daga cikin salihan bayin Allah, a kan haka a irin wannan yanayi dole ne a koma gare su domin sanin ma'anar ayoyi masu kama da juna, wannan ne ya sanya wasu daga cikin masu tafsirin suke karfafawa kan wajabcin sani irin wadannan lamurra kafin yin bayani dangane da kur'ani.
842783