Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, duk da cewa hukumomin kasar Tunisiya sun fara gurfanar da mukarraban hambararren shugaban kasar Zainul Abidin Ben Ali a gaban kuliya amma bisa dukkan alamu jamaa basu gamsu ba domin kuwa a kwanan nan ma an sake yin zanga zanga a birnin Tunis ana rera take mai cewa "Alumma tana bukatar maaikatar shari'a mai zaman kanta."
Wannan zanga zanga ta biyo bayan wanke tsofon ministan sufuri Abdurrahim Zouari da tsofon ministan shari'a Bashir Tekkari da kotu ta yi a makon jiya dangane da tuhumce-tuhumcen da aka yi musu, saboda ta ce bata same su da laifi ba. Ana zargin cewa tsoffin ministocin sun yi amfani da mukamansu sun yi almundahana da dukiyar jamaa. Wani daga cikin mukarraban Zaynul Abidin Ben Ali, wato Saida Agerbi wanda a ke zarginsa da almundahana da kuma yin ayyukan leken asiri wa tsohuwar gwamnatin, an buda masa hanya ya tsere zuwa birnin Paris.
Hakazalika shari'ar da aka yi wa shi kansa Ben Ali da uwargidansa a bayan idonsu, ana ganinta a matsayin wani aikin jeka-na-yika ne kawai saboda hukumar wucin gadin kasar Tunisiyan ta kasa matsa lamba wa gwamnatin Saudiya don ta mika mutanen biyu, wadanda a yanzu haka suke zaune a birnin Jidda na kasar ta Saudiya.
Fiye da watanni shida bayan nasarar juyin juya hali a kasar Tunisiya wanda ya hambare shugaba mai kama-karya Zaynul Abidin Ben Ali, har yanzu tsarin shari'ar kasar ya kasa yin gyararrakin da zasu daukaka mutuncinsa a idanun mutanen kasar.
Hukumar shari'ar ta yanzu ita ce ta yi ayyukan katobara da rashin adalci a zamanin Ben Ali, kuma, a yanzu haka babban bukatar alummar Tunisiya ita ce samar da hukumar shari'a mai zaman kanta da zata iya hukunta tsofaffin jamian gwamnati da ake zarginsu da laifukan cin hanci da rashawa, da kuma wadanda suke da alhakin kashe masu zanga zangar lumana a kwanakin da alumma suka yukura domin kawar da gwamnatin Ben Ali.
Masharhanta dangane da halin da kasar Tunisiya take ciki dai suna ganin cewa da sauran sauran aiki a gaban hukumar wucin gadi saboda kuwa babu alamar cewa alummar kasar zasu zuba ido ana ci gaba tafiya irin ta zamanin Zaynul Abidin Ben Ali.
A sarari yake cewa hukumar shari'a ta kasar Tunisiya ba zata iya gudanar da shari'o'in da zasu gamsar da jamaa ba domin kuwa bata da bambamci da yanda take a zaman hambararren shugaban kasar, saboda haka, kafin ta biya bukatun alummar kasar sai an yi mata garambawul an bata cikakken yanci.
842667