Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, A cikin wadannan ayoyi Alla madaukakin sarki yana yin bayani ne ga manzonsa, tare da ba shi umurni da ya sheda wa wadanda ba su yi imani ba cewa, dukiyoyin da suke takama da su da tarin 'ya'ya da mulki da duk abin da suke ganin ya wadatar da su daga Allah madaukakin sarki,
Duk wannan ba zai amfane su ba, ba zai iya wadatar da su komai daga Allah ba, domin kuwa rashin imani da Allah ya sanya kafiri ya zama abun hura wutar jahannama, a ranar da dukiya da 'ya'ya da karfin iko, ko fada a ji ba su da amfani, sai wanda ya zo ma Allah da zuciya mai imani.
Allah madaukakin sarki yana yi ma muminai bayani cewa; kada su yi zaton cewa a lokacinsu ne kawai aka samu wadanda suka kafirce ma sakon Allah, suka juya fusakunsu daga gaskiya a lokacin da ta zo musu daga ubangijinsu, domin kuwa an yi mutane masu tsananin girman kai da kin gaskiya da zalunci.
Amma daga karshe suka halaka, hatta Fir'auna wanda ya shahara da karfin iko da sarauta da dukiya, daga karshe duk wannan bai amfane shi da komai ba sakamakon rashin imaninsa da sakon Allah da annabi Musa.
844420