IQNA

Wani Kwafin Kur'ani Mai Tsarki Da Aka Danganta Da Imam Ali (AS)

18:58 - August 16, 2011
Lambar Labari: 2172128
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka danganta shi da Imam Amirulmumini Ali Dan Abu Talib (AS) da kuma rubutunsa da cewa nasa amincin Allah ya tabbata a gare shi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani da ke cewa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka danganta shi da Imam Ali Dan Abu Talib (AS) da kuma rubutunsa da cewa nasa amincin Allah ya tabbata a gare shi a wurin baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a nan fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.

Allah madaukakin sarki ya halicci mutum, ya kuma saka shi a bayan kasa, ya sanya wasu abubuwa da dan adam yake bukata domin ci gaba da wannan rayuwa, domin wanzur irin mutum yana bukatar mata da 'ya'ya, domin jin dadin rayuwrsa da biyan bukatunsa na yau da kullum yana bukatar kudi, yana bukatar abin hawa da tufafi da dai sauran abubuwa na bukatuwar dan adam na larura.

Mutum yakan so wadannan abubuwan kamar yadda Allah ya sanya sonsu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma yakan so su fiye da kima, har ma mutum kan iya sanya su tamkar su ne manufar rayuwarsa, ya fifita son mata da 'ya'yansa da dukiyarsa fiye da komai na duniya, har ma da ibadar Allah madaukakin sarki, alhali kuwa ba su ne manufa ta rayur dan adam ba, domin kuwa su ma masu karewa ne a nan gidan duniya.

Kuma dayan biyu, kodai mutum ya barsu, ko kuma su su bar shi, domin kuwa makomar kowa da komai na wajen Allah madaukakin sarki. Idan mutum bai kyautata ayyukansa ba, babu ko daya daga ckin wadannan abubuwan da zai amfane shi a lahira.
844072
captcha