IQNA

18:58 - August 16, 2011
Lambar Labari: 2172129

Bude Wani Shafin Yanar Gizo Domin Hada Ayyukan Ta'addancin sarakunan Bahrain

Bangaren kasa da kasa, an bude wani shafin internet domin tattara bayanai dangane da ayyukan ta'addanci na gidan sarautar kasar Bahrain a kan al'ummar kasar masu neman sauyi cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jam'iyar Alwifaq ta masu fafutuka a kasar Bahrain an bayyana cewa, an bude wani shafin internet domin tattara bayanai dangane da ayyukan ta'addanci na gidan sarautar kasar Bahrain a kan al'ummar kasar masu neman sauyi cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, wadda take cikin yankin gabas ta tsakiya.

A wani labarin na daban kuma, jam'iyar Al-wifaq mai adawa a kasar Bahrain ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki a kasar ta hanyar lumana, duk kuwa da matakan yin amfani da karfi kan 'yan adawa da mahukuntan kasar suke dauka.

A cikin wani bayani da jam'iyar ta Al-wfaq ta fitar jiya, ta bayyana cewa mahukuntan Bahrain da suke samun goyon bayan Amurka da Saudiyya, ba a shirye suke su saurari bukatun al'ummar kasar ba, a kan haka ne ma suke ta kara daukar sabbin matakai na muzguna wa masu neman sauyi a kasar,

Tare da taimakon sojojin Saudiyya da suke jibge a kasar domin murkushe fararen hula masu gudanar da zanga-zangar lumana. Bayanin ya ce jam'iyar ta Al-wifaq na nan kan bakanta na neman a baiwa al'ummar kasar damar gwamnatin da suke so.

A daren jiya ma dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar lumana a garuruwa da daban-daban na kasar Bahrain, inda suka yi Allawadai da gwamnatocin Amurka da Saudiyya, wadanda suke da hannu kai tsaye wajen murkushe yunkurin neman sauyi a kasar.

843933
captcha