IQNA

UNESCO Tana Hada Gwiwa Da Kwamitin Kur'ani Na Kasa Baki Daya

18:57 - August 16, 2011
Lambar Labari: 2172133
Bangaren kasa da kasa, kungiyar UNESCO ta fara gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tare da babban kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasa baki daya, tare da karfafa matasa 'yan jami'a kan harkokin karatu.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani day a naklato daga bangaren hulda da jama'a na reshen kungiyar UNESCO an bayyana cewa, kungiyar ta fara gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tare da babban kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasa baki daya, tare da karfafa matasa 'yan jami'a kan harkokin karatu da kuamsauran lamurra na bunkasa al'ada.

Akasin rayuwar aljanna a lahira, inda Allah ya tanadi dukkanin ni'ima da mutum bai taba yin tunaninta ba, sai dai kawai misali da ake ba shi a cikin kur'ani, domin hankali ya iya riskar cewa akwai ni'ima, amma hakikanin ni'imar aljanna Allah ne kawai ya san yadda take.

Baya ga 'ya'yan marmari masu dadi, da manyan lambuna da koramu ke gudana a karkashinsu, sauran nau'oin abinci da sha, wadanda aka bada misali da su daga cikin ni'imar aljamma, sauran ni'imomin ba musansu, saboda hankalinmu ba zai kama ba, wannan kuma zai ci gaba da kasancewa ne har abada.

Abu mafi soyowa ga 'yan aljanna wanda yafi dukannin wadannan ni'imomi, shi ne yardar Allah madaukakin sarki, a lokacin da suka samu yardarm to sun samu jin dadin da ya fi komai a cikin aljanna.

843740
captcha