Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aimislam an bayyana cewa, mazauna birane daan-daban na kasar Birtania za su gudanar da jerin gwano domin goyon bayan Qods mai alfarma, wanda zai hada kasashen duniya na musulmi da ma wadanda ba nasu ba a cikin gabas ta tsakiya da ma nahiyar turai.
A yammacin jiya ne aka fara gudanar da wata tattaunawa tsakanin jami'an gwamnatocin kasashen Iran da Rasha a birnin Tehran, da nufin kara bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaban majalisar tsaron kasa ta Rasha Nikolay Patrochev shi ne yake jagorantar tawagar kasarsa da ke halartar tattaunawar, yayin da takwaransa na kasar Iran Sa'id Jalili yake jagorantar sauran jami'an Iran a wannan tattaunawa. Kasar Rasha ta bijiro wa Iran da hanyoyi da dama da za su kara bunkasa alakarsu ta diplomasiyya.
Tattalin arziki da kuma batun nukiliya, da kuma batun ci gaba da tattaunawa kan shirin Iran na makamashin nukiliya tare da manyan kasashen duniya, da nufin kawo karshe takaddamar da kasashen yammacin turai suka jawo kan shirin na Iran.
A yau ne bangarorin biyu za su ci gaba da wannan tattaunawa, daga bisani kuma shugaban majalisar tsaron kasa ta Rasha zai gana da shugaba Ahmadinejad, da kuma ministan harkokin wajen Iran din Ali Akbar Salihi. 843586