Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alfurat an bayyana cewa, shugaban majalisar koli ta musulunci a kasar Iraki Sayyid Ammar hakim ya bayyana fim din nan na cin zarafin addinin muslunci ta hanayar keta hurumin iyalan gidan manzon Allah, babban laifi a cikin tarihi na dan adam da aka taba gani.
Kamar dai yadda aka mabata acikin ayar da tag abaci wannan, cewa wasu daga cikin abubuwa na duniya mutum yana sonsu bisa dabi'a, duk kuwa da cewa daga karshe dai masu gushewa ne, amma ita wannan ayar tana yin ishara ne da abubuwa na ni'ima da Allah madaukakin sarki ya yi tanadi ga masu tsoransa a duniya.
wadannan ni'imomi masu dawwama ne na har abada, ba su gushewa saboda tsawon zamani, ko karewa saboda amfani da su, wannan tamkar zabi ne aka baiwa mutum domin ya zabi daya daga cikin wadannan nau'oi biyu na rayuwa, rayuwar duniya mai cike da wahalhalu, bakin ciki, kuma takaitatta. Akasin rayuwar aljanna a lahira, inda Allah ya tanadi dukkanin ni'ima da mutum bai taba yin tunaninta ba.
Sai dai kawai misali da ake ba shi a cikin kur'ani, domin hankali ya iya riskar cewa akwai ni'ima, amma hakikanin ni'imar aljanna Allah ne kawai ya san yadda take. Baya ga 'ya'yan marmari masu dadi, da manyan lambuna da koramu ke gudana a karkashinsu, sauran nau'oin abinci da sha.
Wadanda aka bada misali da su daga cikin ni'imar aljamma, sauran ni'imomin ba musansu, saboda hankalinmu ba zai kama ba, wannan kuma zai ci gaba da kasancewa ne har abada. Abu mafi soyowa ga 'yan aljanna wanda yafi dukannin wadannan ni'imomi, shi ne yardar Allah madaukakin sarki.
844707