IQNA

Har Yanzu Ba A San Makomar Husni Mubarak Na Kasar Masar Ba

17:08 - August 17, 2011
Lambar Labari: 2172830
Bangaren kasa da kasa, har yanzu ba fahimci hakinin lamari dangane da makomar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak ba, domin kuwa kotu ta sanar da dage zaman shari'ar, kuma za adaina watsa ta kai tsaye a talabijin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, har yanzu ba fahimci hakinin lamari dangane da makomar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak ba, domin kuwa kotu ta sanar da dage zaman shari'ar, kuma za adaina watsa ta kai tsaye a kafafen yada labarai.

Yau litinin ne ake ci gaba da gudanar da shara'ar tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak wanda ake tuhumar da bayar da umurnin kashe daruruwan masu zanga-zanga da kuma karkakata akalar dukuiyar kasar mai tarin yawa kafin a kore shi daga kan karagar mulki a cikin watan Fabarairun da ya gabata.

A ranar 3 ga wannan wata ne dai tsohon shugaban kasar wanda ke fama da rashin lafiya ya bayyana karon farko a gaban kotu shi da 'yayansa da kuma wasu tsoffin manyan jami'an gwamnatinsa domin sauraransu dangane da zarge-zargen da ake yi musu.

Akalla dai mutane 850 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu a lokacin da jami'an tsaro masu biyayya ga Husni Mubarak suke kokarin murkushe masu zanga-zangar, kuma a karkashin dokokin kasar ta Masar matukar dai aka sami tsohon shugaban da laifi to lalle ana iya yanke masa hukuncin kisa.



captcha