IQNA

Masu Fasaha Sun Ziyarci Dakin Iqna A Baje Kolin Kur'ani Na Sha Tara

11:42 - August 18, 2011
Lambar Labari: 2173040
Bangaren kasa da kasa, masu fasaha sun ziyarci baje kolin kur'ani mai tsarki da ake guadanrwa yanzu haka a birnin Tehran, inda suke leka dakin kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna da ke wurin.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran an bayyana cewa, wasu masu fasaha sun ziyarci baje kolin kur'ani mai tsarki da ake guadanrwa yanzu haka a birnin Tehran, inda suke leka dakin kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna da ke wurin tun daga lokacin da aka fara gudanar da taron na wannan shekara.

Allah madaukakin sarki ya halicci mutum, ya kuma saka shi a bayan kasa, ya sanya wasu abubuwa da dan adam yake bukata domin ci gaba da wannan rayuwa, domin wanzur irin mutum yana bukatar mata da 'ya'ya, domin jin dadin rayuwrsa da biyan bukatunsa na yau da kullum yana bukatar kudi, yana bukatar abin hawa da tufafi da dai sauran abubuwa na bukatuwar dan adam na larura. Mutum yakan so wadannan abubuwan kamar yadda Allah ya sanya sonsu a cikin zuciyarsa.

Wani lokaci kuma yakan so su fiye da kima, har ma mutum kan iya sanya su tamkar su ne manufar rayuwarsa, ya fifita son mata da 'ya'yansa da dukiyarsa fiye da komai na duniya, har ma da ibadar Allah madaukakin sarki, alhali kuwa ba su ne manufa ta rayur dan adam ba, domin kuwa su ma masu karewa ne a nan gidan duniya, kuma dayan biyu, kodai mutum ya barsu.

Ko kuma su su bar shi, domin kuwa makomar kowa da komai na wajen Allah madaukakin sarki. Idan mutum bai kyautata ayyukansa ba, babu ko daya daga ckin wadannan abubuwan da zai amfane shi a lahira. 845595
captcha