Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, rahoto daga masallacin Imam Khomeini (RA) ya yi nuni da cewa, yanzu haka ana shirin fara gudanar da wani zama kan mikewar musulmi a ckin kasashen larabawa domin 'yanci da sauyi a cikin harkokin siyasar wadannan kasashe, wanda zai gudana a wurin taron baje kolin kur'ani ginin da ke kan masallacin a babban birnin Tehran.
A yayin gudanar da wannan zama, wakilin babbar cibiyar ilimi ta birnin Qom Hojjatol-islam Dr. Zamani zai gabatar da jawabi ga mahalarta taron, danfane da wannan gagagrumin ci gaba da ake samu a halin yanzu a cikin kasashen larabawa da suke fama da shugabanni da sarakuna 'yan mulkin kama karya.
Tun bayan fara wannan bore a cikin kasashen larabawan dai, ya zuwa yanzu shugabanni biyu daga cikin masu mulkin Fir'annci sun bar mulki, da suka hada babban aminin Amurka da yahudawan sahyuniya a cikin kasashne larabawa.
845623