Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, an kawo karshen bangaren baje koli na kayayyakin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa a babban masallacin Imam Khomeini (RA) ada ke birnin Tehran, duk kuwa da cewa ba a gudanar da wani biki na rufe wannan bangare ba kamar yadda aka yi a lokacin bude shi.
Ayar da ta gabata ta yi mana bayani ne kan cew masu taqawa, masu tsoron Allah su ne 'yan aljanna, yayin da ita kuma wannan ayar tana yi mana bayani ne kan dabi'u da halaye irin na masu tsoron Allah, wadanda su ne 'yan aljanna.
Aya ta farko dai tana yi mana bayani ne kan tuba da komawa zuwa ga Allah irn na masu tsron Allah. Ma'anar taqawa ko tsoron Allah ba yana nufin tsarki daga aikata duk wani sabo ba ne, mai tsoron Allah zai iya rafkana ko gafala a wani lokaci ya aikata wani abu wanda laifi ne, zunubi ne.
Duk da cewa ba al'adarsa ba ce aikata irin wannan laifi, sa'annan kuma mai tsoron Allah da aikata wani laifi da ya farga da hakan, a nan take zai koma zuwa ga Allah tare da neman gafararsa, da shiga cikin damuwa saboda ya aikata wani na sabon Allah, kuma zai kiyaye matukar iyawarsa wajen ganin bai kara aikata hakan ba.
Aya ta gaba kuma tana bayyana mana wasu siffofin na masu taqawa, hakuri, gaskiya a cikin akida da zantuka, ta yadda ba za a taba jin suna raki ba saboda wata matsala da duniya, ba za a taba jin karya a cikin zantukansu ba, su masu komawa ne zuwa ga Allah da rokonsa da kaskantar da kai gare shi, masu ciyarwa ne daga abin da suka mallaka, masu yin istigafari ne a karshen dare.
845615