IQNA

An Bayyana Ranar Shahadar Imam Ali (A) Ranar Hutu A Birnin Najaf

11:11 - August 20, 2011
Lambar Labari: 2173739
Bangaren kasa da kasa, an bayyana ranar shahadar Imam Ali (AS) a matsayin ranar hutu a birnin Najaf mai alfarma na kasar Iraki kamar dai yadda mahukunta a birnin suka sanar, wanda shi ne hubbarensa mai tsarki yake a cikinsa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin yanar gizo an bayyana cewa, ranar shahadar Imam Ali (AS) a matsayin ranar hutu a birnin Najaf mai alfarma na kasar Iraki kamar dai yadda mahukunta a birnin suka sanar, wanda shi ne hubbarensa mai tsarki yake a cikinsa wanda kuma al'ummar birnin da sauran masu ziyara suna gudanar da taruka na tunawa da zagayowar ranar.

A wani labarin kuma jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin Gaza, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehmonparest a yau asabar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana Allah wadai da hare haren zalunci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan al'ummar Palasdinu da ke cikin halin azumi a yankin.

Ya fassara manufar kai hare haren da cewar kokari ne kawar da hankulan duniya daga kan matsalolin cikin gida da gwamnatin Natenyahu ke fuskanta, inda ya ce hakan wani kokari na ganin cewa sun dauke hankulan al'umomin duniya dangane da hakikanin abin da ke faruwa.

Har ila yau ya yi kira ga gwamnatocin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da su fito fili su yi Allah wadai da wannan hare haren zalunci, tare da daukan matakin ganin an kawo karshen aiwatar da irin wannan ayyukan ta'addanci a kan al'ummar yankin.
846129


captcha