Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na INGO cewa hukumar bayar da agaji ta kasar Pakistan ta dauki nauyin bayar da buda baki ga marayu akalla dubu biyu da dari hudu a yankin Keshmir da ke karkashin gwamnatin kasar ta Pakistan a daren jiya kamar dai yadda bayanin ya tabbatar.
Wani rahoton kuma yana cewa, Fashewar bom mai karfin gaske a wani masallaci a yankin da ke arewa maso yammacin kasar Pakistan ta yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla 53 tare da jikkata wasu fiye da 130 na daban.
Rahotonni da suke fitowa daga kasar Pakistan suna bayyana cewa: A jiya juma'a bayan taruwan daruruwan mutane domin gudanar da sallar juma'a a yankin Ghandi da ke garin Jumrud a lardin Khaibar da ke yankunan kabilu a arewa maso yammacin kasar Pakistan; wani bom mai karfin gaske ya tarwatse a cikin wani masallaci.
Lamarin da ya yi sanadiyyar rubzawar rufin masallacin a kan jama'a tare da kashe mutane akalla 53 kuma wasu fiye da 130 na daban suka jikkata, kamar dai yadda kafofin yada labarai na cikin gida da kasashen ketare suka tabbatar.
Majiyar lafiya na yankin ta bayyana cewa: Halin mutane da dama daga cikin wadanda suka samu raunuka ya tsananta don haka akwai yiyuwar samun karin hasarar rayuka.
846128