Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, masu gudanar da zanga-zangar lumana a kasar Bahrain sun fara rera taken neman kawo karshen masarautar kasar ta mulkin kama karya, wadda take murkushe yunkurin neman sauyi ta hanyar ruwan sanyi da ake yi a kasar tun kimanin watannai shida da suka gabata.
A lokacin annabawan Allah Musa da Isa da sauran zamunan annabawa, wajibi a kn mutanen wannan zamanin shi ne su yi imani da wannan annabin da abin da ya zo da shi na daga shari'a daga Allah madaukakin sarki, amma bayan aiko manzon Allh Muhammad (SAW) ya zama wajibi na shari'ar ubangiji a kan sauran dukkanin al'ummomin duniya da suke raye a lokacinsa su yi imani da shi.
Hatta ahlul kitabi wajibi ne aknsu su bi abin da manzon allah Muhammad ya zo shi, domin kuwa shi ne shugaban dukkanin annabawa da suka gabata, da wani annabi yana raye a lokacin bayyanar annabi Muhammadu, to da wannan annabi ya zama daya daga cikin mabiyan annabi Muhammadu (SAW) domin kuwa addininsa shi ne ya hada dukkanin addinai na sauran annabawan da suka gabace shi.
Domin daga lokacin bayyana r manzon Allah, duk wanda ya yi wani addini da sunan addinin to ba za akarba daga gare shi ba kamar yadda ayar ta nuna, da kuma yadda muka dan yi Karin haske kan hakan gwarwadon iko. 846119