Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aswatul Irak an bayyana cewa, shugaban jama'ar Sadr a kasar Iraki Sayyid Mukta Sadr ya bayyana cewa, abin da yake faruwa akasar Syria ya banbamta da abin da ya faru a kasashen Masar da Tunisia, inda ya ce Amurka ce ta shirya duk abin da yake faruwa a kasar wadda ta ke kalubalantar Amurka da sauran kasashen yammacin turai.
A bangare guda kuma masu nazari suna ganin Fatattakar kungiyoyi masu dauke da makamai daga garin Lazikiyah na kasar Siriya da jamian tsaron kasar suka yi da kuma sake dawo da zaman lafiya a garin, ya nuna cewa farfaganda da yaki irin na diplomasiya da wasu kasashen Yamma da ma na Larabawa suka kaddamar a kan kasar ta Siriya da zimmar rura wutar zanga-zanga da tarzoma da ake yi a wasu yankunan kasar, ya ci tura. Bayan nasarar da jami'an tsaron kasar Sirirya suka samu ta korar kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai daga garin Dayr al-Zur, a wannan karon kuma sun fitar da irin wadannan jama'a daga garin Lazikiyah kuma hankali ya fara kwanciya a garin.
A tsawon lokacin da garin Lazikiyah yake cikin tashin hankali, masu dauke da makami 'yan ta'adda sun lalata muhimman wurare na hukuma, sannan kuma, ta hanyar tsoratarwa da yin barazana da makaman da suke dauke da su sun firgita jama'a domin tilasta musu shiga zanga-zanga.
Kasashen Yamma da wasu kasashen Larabawa sun yi ta kokarin haddasa tarzoma a garuruwan kasar Siriya kamar Dayr al-Zur, Lazikiyah da kuma Hamah domin adadin mutanen da suke rasa rayukansu da wadanda suke samun raunuka a rikicin ya kara yawa a wadannan yankunan. Kafofin watsa labaran wasu kasashen Yammaci da na Larabawa sun yada hotunan zanga-zanga da taho-mu-gama da ake yi a wannan rikici saboda gurbata tunanin jama'a da kimsa musu kin jinin shugaban kasar Bashar Asad.
Saboda da haka ne wasu kasashen Yammaci mambobi a kwamitin tsaro Majalisar Dinkin Duniya suka yi ishara da tashe-tashen hankali da suke faruwa a Siriya, suka bukaci a dauki tsauraran matakai a kan gwamnatin kasar. Amma kasancewar an sami baraka a tsakanin mambobin kwamitin tsaron, ga kuma yin amfani da hankali da kuma 'yanci da wasu mambobin suka yi, ya sa masu kokarin tunzura kwamitin tsaron, hakarsu ta kasa cimma ruwa.
846523