Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI an bayyana cewa, babban malamin jami'an Azhar ta kasar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa abin da yahudawan sahyuniya na haramtacciyar kasar Isra'ila suke kan al'ummar Gaza ya wuce wuce wuri kuma hakan abin Allawadai ne domin kuwa zalunci ne tantagarya a kan fararen hula da ba su san hawaba blantana sauka.
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa zata yi taron gaggawa a ranar Lahadi don tattauna batun hare haren da HKI ta kai a kan yankin Zirin Gaza cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Tashar talbijin ta kasar Masar ta habarta cewa shugaban hukumar Palasdinawa Mahmud Abbas ya gabatar wa kungiyar da bukatar a yi zaman taro don yin nazari a kan farmakin na Israila a kan Gaza.
Kungiyar kasashen Larabawan mai mambobi 22 zata kira taron gaggawa na wakilan dindindin ka kasashen kungiyar a hedkwatar ta da ke birnin Alkahira.
A ranar Alhamis da ta gabata jiragen saman yakin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila suka fara kai hare haren kan yankin Zirin Gaza, bayan wani hari da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai a matsugunin Eilat na Yahudawa 'yan kaka-gida, wanda ya halaka yan Yahudawan Sahayoniyya takwas.
846703