IQNA

Wani Mahardacin Kur'ani Dan Libya Ne Ya Lashe Gasar Kur'ani Ta Dubai

16:31 - August 21, 2011
Lambar Labari: 2174755
Bangaren kasa da kasa, mahardacin kur'ani mai tsarki dan kasar Libya Khalid Muhammad saleh ne ya lashe gasar harder kur'ani mai tsarki da ak agudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa.



Kamfanin dilalncin labran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Khalee Times an bayyana cewa, mahardacin kur'ani mai tsarki dan kasar Libya Khalid Muhammad saleh ne ya lashe gasar harder kur'ani mai tsarki da ak agudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa a cikin wannan wata na ramadana mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa makarancin ya shiga gaban Abdulalh Hamad Abu Sharidah da kuma Ahmad sari kaya daga kasar Turkiya, wadanda su ne suka kai ga mataki na kusa na karshe, inda ya nuna matukar kwazo, daga karshe dukkanin makarantan suka sallam masa, kamar yadda alkalai suka jinjina masa.

Bisa ga tsarin gasar, wanda ya zio na daya yana samuntsabar kudi har dalar Amurka dubu tamanin, tare da girmamawa ta musamman, inda na biyu zai samu ksan rabin kudin da ya samu, hak dai za a yi laka'ari da matsayi da matakan da mutum ya tsallake.

Mhardacin kur'ani mai tsarki dan kasar Libya Khalid Muhammad saleh ne ya lashe gasar harder kur'ani mai tsarki da ak agudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa wadda aka gudanar a matsayi na kasa da kasa.

846612
captcha