Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato wani rahoto daga jaridar Darul hayat cewa, mutum na biyu a cikin gwamnatin Gaddafi kuma tsohon fira ministansa ya balle ya shiga cikin gungun 'yan tawaye da suke dauke da makamai suna yakarsa tare da taimakon kungiyar tsaro a daidai lokacin da hare-harensu ke ta kara kusantar birnin Tripoli babban birnin kasar.
Tsohon fira ministan kasar Libiya Abdus-Salam Jalloud ya sanar da goyon bayansa ga masu bore a kasar ta Libiya.
Daya daga cikin na hannun daman Mu'ammar Gaddafi shugaban kasar Libiya dan kama karya Abdus-Salam Jalloud ya sanar da bijirewarsa ga gwamnatin Libiya karkashin jagorancin Gaddafi a jiya juma'a, tare da bayyana cikekken goyon bayansa ga Majalisar Wucin Gadi da ke wakiltan masu bore a kasar, kuma a halin yanzu haka ya mika kansa ga masu bore a garin Zintan bayan da ya tsere daga birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya shi da iyalansa.
Abdus-Salam Jalloud ya rike mukamin fira ministan kasar Libiya a shekara ta 1972 zuwa 1977 kuma tsohon mamba ne a Majalisar juyin juya hali da Gaddafi ya jagoranta a shekara ta 1969 da ya kai shi ga mamaye madafun iko a kasar Libiya.
846577