Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah sayyid Isa Qasem ya bayyana cewa shiga cikin zaben cike gurbi na majlaisar kasar Bahrain haramun ne ga dukkanin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah na kasar ta Bahrain.
Shehin malaimin ya ci gaba da cewa, babu halasci gag a wannan zabe a shar'ance, bisa la'akari da rashin halascin hukuncin da ake yi kan al'ummar kasar, domin kuwa hukunci na zalunci da danniya da kuma fira'unanci, wanda mahukuntan kasar suka shahara da shi.
Jagororin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah na kasar Bahrain sun kirayi mabiyansu da su kauracewa wannanzabe na wawantar da hankulan al'ummar kasar, domin kuwa 'yan majalisar da suke wakiltar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a majalisar ne da suka yi murabus za a cike gurbinsu.
Malamin addinin muslunci na kasar Bahrain ya bayyana cewa shiga cikin zaben cike gurbi na majlaisar kasar haramun ne ga dukkanin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah na kasar, ya kuma jaddada cewa kowa ya zama cikin shiri domin tunkarar abubuwan da za su biyi bayan yin watsi da bukatun jama'a.
846482