IQNA

An Jaddada Muhimmanci Tara Taimako ga Al'ummar Kasar Somalia

16:29 - August 21, 2011
Lambar Labari: 2174760
Bangaren siyasa da zamnatakewa, Firaministan kasar Turkiya ya jaddada muhimmancin tara taimako domin taimakon al'ummar kasar Somalia da suke fama da matsanancin fari a wannan shekara.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo fraministan kasar Turkiya ya jaddada muhimmancin tara taimako domin taimakon al'ummar kasar Somalia da suke fama da matsanancin fari a wannan shekara lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

A bangare guda kuma n'ibin limamin masallacin jumma'a a nan ya yi kira ga musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi su tallafawa mutanen kasar Somalia masu fama da yuwwa ya bayyana haka ne a cikin khudubobinsa na jumma'a a yau a massallacin jumma'a da ke nan Tehran.
Na'ibin limamin ya kara da cewa, a halin yanzu cutar cholera da kuma wasu cututtukan suna yaduwa a cikin mutanen kasar masu fama da wannan matsalar. Idan musulmi kadai sun bada tallafin da ya dace babu wanda zai mutu don yuwwa a kasar, inji shi.
A halin yanzu dai jirgin sama daukar kaya na kungiyar Red Cresent ta kasar Iran ya isa birnin Magadushu babban birnin kasar na Somalia dauke da ton 60 na kayakin abinci da kuma magunguna. Kuma wannan shi ne sawunsa na ukku zuwa birnin.
Mutanen kimani miliyon 11.8 daga kasashen Somalia Kenya da Ethiopia ne suke fama da karancin abinci sanadaiyyar rashin ruwan sama da kuma yake yaken da ke faruwa a yankin.
846589

captcha