IQNA

Kasar Venzuella Ta Kori Jakadan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

16:07 - August 22, 2011
Lambar Labari: 2175003
Bangaren kasa da kasa, domin nuna rashin amincewa da hare-hare ta’addancin da sojojin yahudawan sahyuniya suke kaiwa kan al’ummar yankin Gaza marassa kariya, gwamnatin Venzuella ta kori jakadan haramtacciyar kasar Israila da ke kasar.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da ke cewa domin nuna rashin amincewa da hare-hare ta’addancin da sojojin yahudawan sahyuniya suke kaiwa kan al’ummar yankin Gaza marassa kariya, gwamnatin Venzuella ta kori jakadan haramtacciyar kasar Israila da ke cikin kasarta da nufin tabbatarwa haramtacciyar gwamnatin cewa abin da take yi ya sabawa dukaknin ka’idoji na duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wananna mataki bai takaitu da jakadan haramtacciyar kasar ba ne kawai, har ma ya hada da wasu daga cikin jami’an ofishin jakakancin haramtacciyar kasar da suke zaune a birnin Karakaz.
Shugaban kasar ta Venzuella Hogu Chavez ya fito karara ya yi Allawadai da kai harin ta’addancin da yahudawan sahyuniya suke yi kan al’ummar yankin Zirin Gaza marassa kariya, inda ya bayyana hakan da cewa ya sabawa dukaknin dokokin na kasa d akasa, a kan haka ya kamata akame fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila a mika ga kotun manyan laifuka ta duniya ahukunta shi.
A ci gaba da nuna rashin amincewa da hare-hare ta’addancin da sojojin yahudawan sahyuniya suke kaiwa kan al’ummar yankin Gaza marassa kariya, gwamnatin Venzuella ta kori jakadan haramtacciyar kasar Israila da ke kasar ta kudancin Amurka. 847301
captcha