IQNA

Faduwar Shugaban libya Na Daya Daga Cikin Alamun Farkawar Larabawa

12:48 - August 23, 2011
Lambar Labari: 2175513
Bangaren kasa da kasa, faduwar babban shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’ammar Gaddafi na daya daga cikin dalilai na farkawar larabawa bayan kwashe sama da shekaru 40 yana mulkin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, bisa rahotannin da ya samu daga kafofin yada labarai da dama an bayyana cewa Gaddafi ya kama hanyar faduwa, wanda kuma faduwar babban shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’ammar Gaddafi na daya daga cikin dalilai na farkawar larabawa bayan kwashe sama da shekaru 40 yana mulkin kasar ta Libya, inda dubban mutane suka fito suna ta shewa suna murna a wasu yankuna na birnin Tripoli bayan isar ‘yan tawaye.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dai ‘yan tawayen kasar ta Libya da suke dauke da makamai sun samu nasarar shiga birnin na Tripoli, kuma suna ci gaba da nausawa zuwa yankin babul aziziya inda nan mazaunin Gaddafi tare da mukarrabansa.
Wasu rahotannin sun tabbatar da cewa yanzu haka dai dansa da ya fi bayyana akafafen yada labarai Saiful Islam ya shiga hannun ‘yan tawayen, kuma suna tsare da shi tare da kanensa Muhammad Gaddafi, daga bisani za a san makomarsu.
Kasar Libya dai ta fara fuskatar bore ne bayan da aka kjawar da gwamnatin mulkin kama karya ta tsohon shugaban kasar Tunisia, inda mutane suka mike domin tabbatar da manufarsu ta neman sahihin mulki a cikin kasashensu.
847906

captcha