Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, a daren yau ne za agudanar da wani zama na tattauna hanyoyin tarjamar littafan addinin muslunci da kuma tafsirin kur’ani mai tsarki a wurin taron baje kolin kur’ani da ke gudana a karo na goma sha tara 19 a nan birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci.
Kowane manzon Allah da Allah madaukakin sarki ya aiko yana da wata mu’ujiza da yake nuna wa mutanensa domin gajiyar da su kan sakon Allah, amma mu’ujizar manzon karshe tsira da amincin su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ita ce kur’ani mai tsarki.
Allah ya kirayi masu musun muslunci da kur’ani da su kawo wani littafi da ya yi kama da kur’ani sai a kwatanta a gani, ba za su iya kawo wani makamncinsa ba, koda kuwa aya daya ce da ta yi kama da ayar kur’ani mai tsarki, domin kuwa lafazin kur’ani ba lafazi ne na mutum ba, bai ma yi kama da lafazin abin halitta ba.
847870