IQNA

Taron Fadakar Da Iyali Kan Koyarwar Kur’ani A Baje Koli Na Goma Sha Tara

12:48 - August 23, 2011
Lambar Labari: 2175520
Bangaren zamantakewa, ana shirin gudanar da wani zamna taro kan fadakar da iyali dangane da matsayin yin aiki da koyarwar kur’ani mai tsarki a cikin dukaknin lamurra na rayuwa, daidai da yadda muka gani a cikin darasin da suratul insan take koyar da mu.

Wannan taro dai zai gudana ne a babban masallacin birnin Tehhran tare da halartar iyalai da dama, dukkanin masana na duniya sun tafi kan cewa kur’ani babbar mu’ujiza ce manzon Allah ya zo da ita, domin kuwa kur’ani mai tsarki ya bayar da bayanai dangane da annabawa da suka gabata, da abubuwan da suka faru tun daga lokacin halittar annabi Adamu da sauran annabawa, har zuwa lokacin da manzo ya bayyana da sakon Allah madaukakin sarki a hijaz.
Kamar yadda muka fada kowane annabi daga cikin annabawan Allah ya kan zo da mu’ujiza da za ta tabbatar da cewa abin da ya zo da shi ba daga gare shi yake ba, sako ne daga Allah mahaliccin kowa da komai, kuma mun bayyana cewa sakon kur’ani daga Allah shi ne mu’ujizar manzon Allah Muhammad dan Abdullah (SAW) Za mu kawo abubuwa kamar hudu dangane da hakan.
847866



captcha