IQNA

Fasahar Musulunci Na Da Matukar Muhimmanci A Fadakar Al'ummar Musulmi

14:30 - August 24, 2011
Lambar Labari: 2176237
Bangaren kasa da kasa, ayyukan fasahar musulunci na da matukar muhimmanci da tasiri a wajen fadakar da al'ummomin musulmi da na larabawa, inda aka yi amfani da irin wannan hanaya a wasu kashen da suke fuskatar zalunci daga shugabanninsu a cikin kasashen larabawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ayyukan fasahar musulunci na da matukar muhimmanci da tasiri a wajen fadakar da al'ummomin musulmi da na larabawa, inda aka yi amfani da irin wannan hanaya a wasu kashen da suke fuskatar zalunci daga shugabanninsu a cikin kasashen larabawa lamarin da ya yi gagarumin tasiri.

Allah Madaukakin sarki yana ba kafirai rata a cikin abin da suke yi na kafrci, wannan kuma sunna ce ta Allah, wannan kuwa ba gazawa ce daga Allah ba, a'a yana ba su dama ne domin su yi abin da suke so, su yi girman kai su yi jiji da kai, su yi kafirci da fitsara a bayan kasa, ta yadda Allah zai kama su da hujja, wanda hakan ke tabbatar da adalci irin na Allah.

Domin kuwa da a ce lokacin da suke cikin kafircinsu za su dawo su tuba su kadaita Allah, su bi manzonsa, to da Allah ya gabatar musu dukkanin abin da suka yi masa na manyan laifuka.

To amma kafirai da suke cikin duhun dimuwa, suka yi nisa da hasken shiriya, suna ganin hakan tamkar gazawa ce daga Allah, domin kuwa ya ce kada a yi kaza, su kuma sun yi wannan abun ba tare da wani abu ya same su ba, wannan sai ya kara nisantar da su hasken imani, tare da kara nutsewa a cikin bata da duhun kafirci da shirka.

847572
captcha