Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalt daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, iyalan Imam Musa Sadr sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin kira ga 'yan tawayen kasar Libya da suka kawar da Gaddafi da su binciki batun mai gidan nasu wanda ya bata bayan gayyatar da hambararren shugaban kasar ya yi masa wanda kuma tun daga wancan lokacin ba a sake jin duriyarsa ba har inda yau take.
A bangare guda kuma Yan tawayen kasar Libya sun bada labarin kwace iko da babban filin sauka da tashin jiragen sama na babban birnin kasar Tripoli.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ne ya bayyana wannan labarin a daren jiya asabar, kuma ya kara da cewa ana jin karar tashin boma bomai da kuma aman wutan bindigogi a kusan ko ina a cikin birnin.
Labarin ya kara da cewa tun lokacinda yan tawayen suka sami iko da garin Zawiyya mai muhimmanci, sojojin kazzafi basa nuna wata turjiya mai yawa a gaban yan tawayen sai su gudu.
A farko farkon tawayen dai, a cikin watan Febreru da ya gabata, mutanen garin Zawiyya sun gudanar da zanga zangar nuna kiyayya ga mulkin shugaba Gazzafi amma sojojinsa suka murkushesu da manyan bindigogi.
Har'ila yau garin Zawiyya ce kadai babban hanyar fita daga kasar ta kan iyakarta da kasar Tunisia. Kuma tana da babban matatar mai wanda ke bada makamaci mai yawa ga babban birnin kasar.
Har'ila yau a wani labarin kuma gwamnatin kasar Tunisia ta amince komitin gudanarwa na yan tawayen kasar ta Libya mai mazauni a birnin Bengazi a matsayin halattaciyar gwamnatin kasar ta Libya a jiya asabar.
848173