Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ta bukaci sanin makomar Imam musa Sadr da kuma wurin da ake tsare da shi a cikin kasar Libya, haka nan kuma ta bukaci 'yan tawayen kasar da su yi baynai da kan makomarsa da batunsa wanda ya kwashe shekarukimanin talatin da uku 33 ana ta kai komo a kansa.
Wani bayanin kuma ya ce an bayyana cewa, iyalan Imam Musa Sadr sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin kira ga 'yan tawayen kasar Libya da suka kawar da Gaddafi da su binciki batun mai gidan nasu wanda ya bata bayan gayyatar da hambararren shugaban kasar ya yi masa wanda kuma tun daga wancan lokacin ba a sake jin duriyarsa ba har inda yau take duk kuwa da cewa akwai amsu zaton cewa yana raye.
Shi kuwa shugaban kasar Libya Mu'ammar Khaddafi ya yi alkawalin ci gaba da yaki ba tare da ja da baya ba, a wani jawabin da tashar telbjjin din 'al'urubah' ta watsa dazu, shugaba Mu'mmar Khaddafi ya ce janyewa daga fadar gwamnati ta fadar Aziziyya wata dabara ce ta yaki, sannan kuma ya jaddada cewa ba zai mika wuya ba.
Shugaba Mu'ammar Khaddafi ya ci gaba da cewa zai yi gwagwarmaya da dukkan karfin da ya ke da shi akan wadanda ya kira masu wuce gona da iri ko ya yi nasara ko kuma ya yi shahada.
Khaddafi ya ci gaba da cewa kungiyar tsaro ta Nato ta riga ta yi raga-raga da fadar Babul Aziziyya saboda hare-hare har guda 64 da su ka kai mata.
A jiya talata ne dai masu adawa da gwamnatin Khaddafi su ka kutsa cikin fadar Babul-Aziziyya bayan fada mai tsanani da masu kare gwamnati, sannan kuma su ka daga sabuwar tutarsu akan saman fadar.
848149