Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato rahoto daga shafin sadarwa na tashar talabijin din al'alam cewa, kungiyar 'yan uwa musulmi ta kasar Masar ta taya 'yan tawayen kasar Libya murnar samun nasara a kan shugaban mulkin kama karya na kasar Mu'ammar Gaddafi tare da dukkanin sauran al'ummar kasar ta Libya wadda ta kwashe tsawon shekaru karkashin mulkin zalunci da danniya.
A wani bangare kuma a daidai lokacin da 'yan tawayen kasar Libya suka sanatr da cewa sun shiga birnin Tarabulus da kuma yiwuwar su sami cikakken iko kan birnin, kasashenn yamma suka fara bayyana kwadayinsu kan dumbin arzikin man fetur da iskar gas da kasar ta mallaka. Mai magana da yawun kamfanin Total na kasar faransa ya fadi a ranar Litinin cewa kamfanin yana lura da sauye-sauyen da suke faruwa a kasar ta Libya kuma yana nazarin yanda za ya sami kwangilar fitar da man fetur a lokacin da ya dace.
Ministan harkokin wajen kasar Italiya, Franco Fratinni ya ce: a yanzu haka kamfanin Eni na kassarsa yana tattaunawa dahukumar wucin gadi dangane da sake gina wuraren aikin mai na kasar Libya, kuma ya bai wa kamfanonin kasar Italiya tabbacin cewa gwamnatin da za a kafa a nan gaba a kasar ta Libya zata mutunta dukkanin yarjejeniyoyion da aka sanya wa hannu tsakanin tsohuwar gwamnati da kamfanonin.
Joseby Ritchi babban darektan gudanarwa a kamfanin Eni ya ce aiki tare da kasar Italiya zai bai wa Libya damar dawo da ayyukan fitar da mai da isakr gas kamar yadda ya kamata kafin lokacin dari ya shigo kamfanin British Petroleum na kasar Biritaniya ma ya sanar da cewa da zarar jami'an hukaumar wucin gadin Libya sun amince, kamfanin zai fara ayyukansa a kasar gadan-gadan.
848195