IQNA

Zaman Tattaunawa Kan Batun Kasar Libya A Birnin Istanbul

16:21 - August 24, 2011
Lambar Labari: 2176281
Bangaren kasa da kasa, kasashen da suke da hannu wajen kaddamar da yaki kan al'ummar kasar Libya da nufin kawar da shugaban kasar Mu'amar Gaddafi za su gudanar da zaman tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na maktoob an bayyana cewa, kasashen da suke da hannu wajen kaddamar da yaki kan al'ummar kasar Libya da nufin kawar da shugaban kasar Mu'amar Gaddafi za su gudanar da zaman tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar bayan nasarar da 'yan tawaye da suke dauke da makamai suka sau.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zama yana da muhimmanci ga wadannan kasashen musamman ma na turai daga cikinsu, tun kafin yakin kasar Libya ya kawo karshe, tuni kamfanonin man fetur da iskar gas na kasashen yamma sun fara gasa kan cin moriyar dumbin arzikin kasar Libya na wannan fanni.

Kyakkyawan nau'in man na Libya da kusancin wuraren aikin man kasar da gabar tekun Mediterraniya su suka kara kwadayin kasashen yamma na samun man Libya. Bayan watanni shida cur ana fafatawa, a yanzu da ake ganin masu juyin juya hali a kasar Libya zasu karbi ragamar shugabancin kasar baki daya.

Muhimmin abin da al'ummar kasar suke bukata shi ne tabbatar da kwanciyar hankali da sake gina kasarsu, kuma suna fatar kasashen waje zasu taimaka musu a wannan gagarumin aiki, amma bisa dukkan alamu wata manufa ta daban ce kasashen Yammaci suke da ita.

Wadannan kasashen da suke da hannu wajen kaddamar da yaki kan al'ummar kasar Libya da nufin kawar da shugaban kasar Mu'amar Gaddafi za su gudanar da zaman tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar ta Libya. 848277
captcha