Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na al'alam an bayyana cewa, tasirin tarukan ranar Qods da ake gudanarwa a kowace shekara na ci gaba da bayyana a cikin kasashen musulmi bayan kwashe tsawon shekaru ana zaluntar al'umamr wanna yanki a hannun manyan masu girman kai na duniya baki daya, kamar dai yadda hakan ta tabbata a zahiri.
Daga cikin irin bayanan da ake ta watsawa a kasashen duniya, yanzu an fara shirin gudanar da taruka da kuma gangami na ranar Qods a sassa na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ba na musulmi ba, wanda zai gudana gobe Juma'a ta karshen watan Ramadan mai alfarma kamar yadda mariyagayi Imam Khomeini (RA) ya ayyana a lokacin da yake raye, kuma tun daga lokacin ne ake gudanar da tarukan wanna rana.
Nasarar juyin juya halin muslunci na Iran wanda ya kasance tun kimanin shekaru talatin da uku da suka gabata, ya yi babban tasiri wajen fadakar da al'ummar musulmi dangane da halin da ake ciki na zaluncin kasashe masu girman kai, da kuma munafukai daga cikin gwamnatocin kasashen musulmi da na larabawa wadanda ba su boye hakan ga kowa.
Yana daga cikin muhimamn abubuwa da wannan juyin juya hali ya gadawar al'ummar musulmi, musamman ma wadanda ake zalunta daga cikinsu, kuma amfanin hakan zai koma ne ga dukkanin al'ummomi, musulmi da wadanda ba musulmi ba da suke fuskatar zalunci daga kasashen duniya masu girman kai da kuma munafukai akmar dai yadda muke gani a wannan zamani.
849122