Bangaren kasa da kasa, ranar Qods ta duniya a wannan karo ta sha banbam da sauran makamantanta da ake gunarwa a sauran shekarun da suka gabata, domin kuwa ta z one daidai lokacin da ake gudanar da bore a cikin kasashen larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, da dama daga cikin malamai da masana suna ganin cewa ranar Qods ta duniya a wannan karo ta sha banbam da sauran makamantanta da ake gunarwa a sauran shekarun da suka gabata, domin kuwa ta z one daidai lokacin da ake gudanar da bore a cikin kasashen larabawa day a kai ga faduwar wasu daga cikin muggan munafukai daga cikinsu.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin al'alam an bayyana cewa, limamin masalacin garin Saida kuma daya daga cikin fitattun manyan malaman addini a kasar Lebanon ya bayyana ranar qods a matsayin ranar yin fada da girman kan manyan kasashen duniya baki daya ba kawai yahudawan sahyuniya ba bisa la'akari da cewa dukaknin ayyukan zalunci da suke yi hakan na kasancewa ne karkashin goyon bayan da suke samu daga irin wadannan kasashe musamamn uwar shaidanu.
Wasu daga cikin wawayen larabawa suna bayyan irin wannan yunkuri da cewa ba komai ba ne illa hankoron da Iran take yi wajen ganin ta mamaye komai a cikin harkokin larabawa, inda suke bayyana batun palastinu da cewa lamari ne na larabawa kawai da ba shi da wata dangantaka da musulmi.
848990