IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Kai Hari Kan Masu Buda Baki A Lebanon

10:52 - August 25, 2011
Lambar Labari: 2176581
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ta yi kakkausar suka dangane da kai harin ta'addancin da aka yi kan masu gudanar da taron buda baki a garin Akkar da ke arewacin kasar Lebanon.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar da ke Lebanon an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ta yi kakkausar suka dangane da kai harin ta'addancin da aka yi kan masu gudanar da taron buda baki a garin Akkar da ke arewacin kasar, wanda wasu mutane suka kai a giadan daya daga cikin fitattaun malaman addinin muslunc na yanki, wanda hakan ya fuskanci kakkausar suka daga bangarori daban-daban na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kungiyar hzibullah tana kallon wannan harin ta'addanci wanda ya yi sanadyar rasuwar daya dag acikin mahalrat buda bakin, tare da jikaktar wasu ba komai ba ne illa kokarin ganin an haifar da matsala ta bangaranci da mazhabci da abin da ya yi kama da hakan.

Daga karshen bayanin kungiyar ta kirayi dukaknin al'ummomin kasar Lebanon da su zam acikin fadaka kan yunkurin da awasu da aka baiwa kwangila suke yi, na ganin dun kawo rarraba da rashin fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar, bugu da kari kuma su kawo baraka da rashin digaro da gwagwarmayar al'ummar kasar.

848918





captcha