IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Taya Al'ummar Libya Murnar Samun Nasara

10:53 - August 25, 2011
Lambar Labari: 2176582
Bangaren kasa da kasa, kungiyar raya harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ta taya al'ummar kasar Libya murnar samun nasara kan kawar da Gaddafi daga shugabancin kasar na tsawon shekaru sama da arba'in.

Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, kungiyar raya harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ta taya al'ummar kasar Libya murnar samun nasara kan kawar da Gaddafi daga shugabancin kasar na tsawon shekaru sama da arba'in yana yin abin da ya ga dama a kasar.

A nata bangaren ma kasar Chadi ta amince da majalisar 'yan tawayen Libya, inda Ministan harkokin wajen kasar ta Chadi Musa Dago ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ta amince da hukumar wucin gadin kasar Libya a matsayin hukama mai halasci a kasar.

Musa Dago ya yi wannan bayani a gaban wakilai shida na hukumar wucin gadin Libyan da suka kai ziyara wa shugaban kasar Chadi Idris Derby Itno tun a ranar Litinin.

Ita ma kasar Habasha ta bayyana aminewarta da hukumar wucin gadin ta Libya a yau. Kakakin gwamnatin kasar Dina Mufti ya sheda wa manema labarai a birnin Adis Ababa cewa Habasha ta amince da hukumar ta Libya ne tare wasu kasashe.

Dina Mufti ya yi wannan bayani ne a taron yan jarida da ministocin harkokin wajen Habasha da Najeriya suka kira a birnin Adis Ababa a yau. Tun a jiya Talata ne dai Najeriya ta sanar da amincewarta da hukumar yan tawayen na Libya.

848863




captcha