IQNA

'Yan Tawayen Libya Sun Saka Wa Gidan Gaddafi Sunan Gidan Tsayuwa

10:53 - August 25, 2011
Lambar Labari: 2176584
Bangaren kasa da kasa, 'yan tawayen kasar Libya sun saka wa gidan Gaddi sunan gidan dakewa bayan da suka mamaye yankin babul aziziya inda nan gidan yake da sauran wurare da jami'an gwamnatinsa suke zaune.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin da 'yan tawayen kasar Libya suka sanatr da cewa sun shiga birnin Tarabulus da kuma yiwuwar su sami cikakken iko kan birnin, kasashenn yamma suka fara bayyana kwadayinsu kan dumbin arzikin man fetur da iskar gas da kasar ta mallaka. Mai magana da yawun kamfanin na kasar faransa ya fadi a ranar Litinin cewa kamfanin yana lura da sauye-sauyen da suke faruwa a kasar ta Libya kuma yana nazarin yanda za ya sami kwangilar fitar da man fetur a lokacin da ya dace.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya, Franco Fratinni ya ce: a yanzu haka kamfanin Eni na kassarsa yana tattaunawa dahukumar wucin gadi dangane da sake gina wuraren aikin mai na kasar Libya, kuma ya bai wa kamfanonin kasar Italiya tabbacin cewa gwamnatin da za a kafa a nan gaba a kasar ta Libya zata mutunta dukkanin yarjejeniyoyion da aka sanya wa hannu tsakanin tsohuwar gwamnati da kamfanonin.

Babban darektan gudanarwa a kamfanin Eni ya ce aiki tare da kasar Italiya zai bai wa Libya damar dawo da ayyukan fitar da mai da isakr gas kamar yadda ya kamata kafin lokacin dari ya shigo domin gudanar da ayyukansa.

849015

captcha