IQNA

Batun Palastinu Batu Ne Da Ya Yi Kama Da Sallarmu Da Azuminmu

15:27 - August 27, 2011
Lambar Labari: 2177567
Bangaren kasa da kasa, batun palastinu batu ne da ya yi kama da sauran bangarori na addinin muslunci da za su rabu ba, domin kuwa da hakan ya hada da salla da azumi saboda Qods ita ce alkiblar farko ta musulmi kuma palastbiwa musulmi ne da suke fuskantar kisan kiyashi daga makiya Allah.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tasjar talabijin din Almanar ta kasar Lebanon an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa batun palastinu batu ne da ya yi kama da sauran bangarori na addinin muslunci da za su rabu ba, domin kuwa da hakan ya hada da salla da azumi saboda Qods ita ce alkiblar farko ta musulmi kuma palastbiwa musulmi ne da suke fuskantar kisan kiyashi daga makiya Allah da suke yaki da Allah da addininsa gada-gadan, wato yahudawan sahyuniya.

Ya ci gaba da cewa dole ne kowane musulmi ya ji a cikin jikinsa cewa lamarin masallacin Qods ya shafi addininsa kai tsaye, kuma jefa wannan masallaci da al'umamr musulmi da suke zaune a cikin wannan yanki babban hadari ne ga musulmi da musulunci, day a rataya kan dukaknin musulmin duniya su bayar da gudunmawa wajen kare wannan masallaci da al'uuamr palastinu.

Dangne da tarukan ranar Qods ta duniya kuwa, ya bayyana cewa, hakan na da gagarumin tasiri wajen fadakar da al'ummar musulmi da sauran mutanen duniya wajen sanin halin da ake ciki a yankin palastinu, da kuma irin tabargazar da yahudawan sahyuniya suke tafkawa.

Sayyid Hassan Nasrullah dai shi ne jagoran kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon da ta fattaki yahudawan sahyuniya a loakcin yakin da ta kaddamar a kan al'ummar Lebanon a shekarun baya.

850093

captcha