Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-tagheer an bayyana cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Yemen sun fitar da wani bayani da ke cewa, ranar qods ta duniya ita ce ranar da dukkanin mutanen da ake zaluncta aduniya ya kamata su yi amfani da ita domin samun 'yanci da fita daga danniyar zaluncin masu girman kai an duniya baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa A yau juma'a ne aka gudanar da zanga-zangar ranar qudus ta duniya acikin kasashe da dama, a nan jamhuriyar musulunci miliyoyin mutane ne su ka fito kan tituna acikin birane da kauyuka suna masu bada taken yin Allah wadai da ci gaban mamayar da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta ke yi wa palasdinu.
An kuma gabatar da jawabai tare da fitar da bayanai da su ke jaddada muhimmancin hadin kan al'ummar musulmi domin 'yanto da masallacin qudus da kuma palasdinu.
A kasar Masar mutane miliyan guda ne su ka yi cincirindo a bakin ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra'ila suna masu kira da a yanke huldar jakadancin ya gwamnatin shayoniya.
A kasar Tunisiya an yi taro tunawa da ranar ta qudus irinsa na farko a tarihin kasar inda aka gabatar da jawabai na jinjinawa gwagwarmayar palasdinu.
A kasar Lebanon shugaban kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasarallah ya gabatar da jawabi a garin Marunar-ras tare da jaddada hakkin palasdinawa akan kasarsu ta palasdinu.
A arewacin Najeriya ma an gudanar da zanga-zanga acikin manyan biranen arewacin kasar cikin bada taken 'yanto palasdinu daga mamaya.
849910