IQNA

Masu Gangami A Masar Sun Bukaci A Kori Jakadan Isra'ila Daga Kasar

16:48 - August 28, 2011
Lambar Labari: 2178208
Bangaren kas ada kasa, matasan da suka gudanar da gangamin ranar Qods a birnin Alkahira na kasar sun yi kira ga majalisar sojin kasar da ta gaggauta korar jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabe ta kasar Masar an bayyana cewa, matasan da suka gudanar da gangamin ranar Qods a birnin Alkahira na kasar sun yi kira ga majalisar sojin kasar da ta gaggauta korar jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin tun bayan yarjejeniyar da aka kulla ta sulhu tsakanin gwamnatin masar da Isra'ila shekaru kimanin talatin da 'yan kai da suka gabata.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wani bayanin kuma ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya sanar da cewa; haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince kasar Masar ta jibge sojoji masu yawa a tsibirin Sina mallakin kasar ta Masar ba.
Jaridar Ha'aretz a shafinta na Internet ta bayyana cewar a jiya asabar ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Ihud Barak ya sanar da cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince da shirin kasar Masar na jibge sojoji masu tarin yawa a tsibirin Sina da ke kusa da kan iyaka da Isra'ila ba.
A gefe guda kuma Mujallar Economist da ake bugawa a kasar Birtaniya a fitowarta ta ranar Juma'a ta bayyana cewa; Ihud Barak ya furta cewar idan gwamnatin Masar zata jibge sojojin masu yawa a tsibirin na Sina da nufin magance tashe tashen hankula da suke faruwa a kan iyakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila ce, to babu matsala zata iya jibge sojojin domin hakan zai zame amfani ne ga Isra'ila.
850492

captcha