IQNA

Dubban Daruruwan Palastinawa Ne Suka Yi Salla A Masallacin Qods

16:53 - August 28, 2011
Lambar Labari: 2178210
Bangaren kasa da kasa, dubban daruruwan palastinawa ne suka gudanar da sallar juma'a acikin masallacin qods duk kuwa da irin tsauraran matakan da sojoji da jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka na hana su yin sallar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na CPI an bayyana cewa, dubban daruruwan palastinawa ne suka gudanar da sallar juma'a acikin masallacin qods duk kuwa da irin tsauraran matakan da sojoji da jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka na hana su yin sallar a ranar wadda ta yi daidai da ranar qods ta duniya.
Ita kuwa gwamnatin kasar Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafin kudaden da take bawa gwamnatin Palasdinawa idan har ta gabatar da bukatar kafa kasar Palasdinu ga babban zauren cikin wata satumba mai zuwa, daniel rubinstein, karamin jakadan Amurka a birnin Qudus ne ya bayyana haka wa gidan television na al-jazeera ta turanci.

Rubinstein ya kara da cewa, duk wata bukata ta kafa kasar Palasdinu wacce babban zauren za ta aikewa komitin tsaro na majalisar kasar Amurka zata yi palatali da shi.
Da dama daga cikin yan majalisar dokokin Amurka, daga jam'iyyun Republicans da kuma Democrats duk sun yi barazanar dakatar da tallafin kudaden da gwamnatin jam'iyyar Fata ta Mahmood Abbas take samu daga kasar Amurka matukan ta gabatar da bukatar kafa kasar Palasdinu a.

Fiye da gwamnatocin kasashen duniya 100 ne suka amince da kasar Palasdinu mai iyakoki kafin yakin kwanaki 6 na shekara 1967. Yankunan kasar Palasdinu a lokacin dai sun hada da Yammacin Kogin Jordan, Yankin Gaza, da kuma gabacin birnin Qudus.

Kafin wata kasa ta samu karbuwa a dai tana bukatar yardar akalla kashi 2/3 na wakilan kasashen duniya a babban zauren majalisar- wato akalla kasashe 128, sanna daga karshe dole ne ta sami amincewar komitin tsaro na majalisar.
850449

captcha