Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ThePeninsula cewa, dubabn mata da kanan yara ne suka shiga cikin gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki ta kasar Qatar wadda aka kammala a ikin daren jiya tare da halartar wasu daga cikin wakilan cibiyoyin ilimi da na kur'ani mai tsarki na kasar, da ma wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka halarci wurin.
Kamar yadda muka fada a cikin bayanin ayar da ta gabata, manzon Allah (SAW) ya umurci dukkanin musulmi da suka halarci yakin Uhud da su kara daura damara domin tunkarar rundunar mushrikai da suke nufin afkawa birnin madina, hakan ya sanya hatta wadanda suka ji raunuka ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da wannan umurni na manzo.
Hakan ya jefa tsoro mai tsanani a cikin zukatan kafirai, inda suka ja baya, bayan sun kudiri aniyar yin kisan gilla a kan muslmi a cikin birnin Madina. Sai wannan ayar ta safka, domin yaba wa musulmi da kuma jaruntar da suka nuna.
Wannan ayar tana koyar da mu wani babba darasi, shi ne cewa idan musulmi suka san abin da ya rataya kansu kuma suka yi aiki da umurnin Allah, to za su samu taimakon ubangiji a cikin dukkanin halin da suka samu kansu na tsanani.
850403