IQNA

Shigar NATO A Cikin Libya Ya Rage Armashin Juyin Al'ummar Kasar

16:51 - August 28, 2011
Lambar Labari: 2178213
Bangaren kasa da kasa, limamin masallacin juma'a na yankin Katif a kasar saudiyya ya bayyana cewa, shigar da dakarun tsaron na kasashen turai wato nato suka yi cikin harkokin kasar Libya hakan ya rage armashin juyin juya halin da mutanen kasar suka yi da jininsu.




Kamfanin dilancin labaran iqna ya hbarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, limamin masallacin juma'a na yankin Katif a kasar saudiyya ya bayyana cewa, shigar da dakarun tsaron na kasashen turai wato nato suka yi cikin harkokin kasar Libya hakan ya rage armashin juyin juya halin da mutanen kasar suka yi da jininsu da rayukansu, amma abin ban takaici kasashen yamacin turai wadanda su kansu makiya ne ga al'ummar Libya, sun yi ruwa su tsaki a cikin lamarin baki daya.

A bangare guda kuma an gano gawawwakin mutane hamsin da aka kona a cikin wani gidan kurkuku da ke kusa da Tripoli babban birnin kasar Libya, a jiya asabar ne majiyar yan tawayen Libya ta sanar da cewa an gano gawawwakin ne a yankin Salahud-Din mai nisan kilo mita biyar daga birnin Tripoli.

Rahonni na nuni da cewa mayakan da su ke biyayya ga hambararren shugaban kasar Mu'ammar Khaddafi ne da su ka sha kashi a hannun 'yan tawaye acikin wannan yankin su ka kona mutanen da su ke rike da su a yayinda su ke janyewa.

Daya daga cikin 'ya'yan Khaddafi mai suna Khamis wanda kuma kwamanda ne na rundunar soja mafi girma, sansaninsa ya kasance a cikin wannan yankin na Salahud-Din, kawo ya zuwa yanzu kaso 95% na birnin Tripoli yana hannun 'yan tawayen na kasar ta Libya.


850392

captcha