Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo romandie an bayyana cewa, limamin jumar birnin Tripoli na kasar Libya ya bayyana a cikin hudubar salla cewa juyin da mutanen kasar suka yin a neman 'yanci da musulunci ne, bayan da sua jwashe shekaru sama da araba'in da biyu suna karkashin mulkin danniya da zalinci da kama karya na Mu'ammar gaddafi.
Kasar Libya tana cikin lokaci mai rikici da sarkakiya. A gefe guda masu juyi suna kokarin kama Muammar Gaddafi da yayansa domin gurafanar da su a gaban kotu. A wani gefen kuma, domin tabbatar da dukkan iko ya na hannun sabuwar hukumar wucin gadi, mayakan juyin juya hali suna fafutukan tsarkake garuruwa da biranen kasar daga sojan hayan da hambararren shugaban ya yi amfani da su wajen yakar masu masa tawaye. Har wala yau wani babban aikin da ke gaban hukumar wucin gadi shi ne kafa gwamnatin rikon kwarya wacce zata jagoranci kasar Libya wajen samar da sabon tsarin siyasa da hukumomin demokiradiya.
A wannan yanayi muhimmin aikin da ke gaban sabuwar hukumar shi ne tattaro kawunan dukkan kungiyoyi masu adawa da Gaddafi a karkashin inuwa guda. Dangane da haka ne wani babban kwamandan sojojin juyin na Libya Abdulhakim Balhaj ya sanar a wani taron manema labarai a birnin Tarabulus a ranar Jumaa cewa an hado kan kungiyoyi mayaka daban daban a karkashin shugabancin majalisar soji daya tilo.
Idan aka yi laakari da tsarin zaman alumma a kasar Libya wanda ya ke tafiya bisa tsarin kabilu, hado kan mayakan wadanda suka yi adawa da Gaddafi zai taimaka wajen hana rarrabuwar kawuna tsakanin bangarorin alumma. Ko da yake akasarin kabilun Libya sun goyi bayan kawar da Gaddafi amma da akwai tsoron cewa ko wace kabila zata bukaci kaso a sabuwar gwamnatin da zata akafa a nan gaba, kuma hala hakan ya jawo rikici. Saboda gujewa wannan tunani na yin gasa tsakanin kabilu, hukumar wucin gadi take kokarin hada mayakan kabilun yammacin kasar da gabashin kasar a karkashin shugabanci ko kuma iko daya.
850335